Babu Alamar Za'a Yi Zaben Kananan Hukumomi A Jihar Kano

Dr. Abdullahi Umar Ganduje Gwamnan Kano

Wa'adin shugabannin kananan hukumomin Jihar Kano arba'in da hudu zai cika wannan watan amma babu alamar hukumar zabe zata shirya sabon zabe kafin nan da karshen wata

A karshen wannan watan Mayu ne wa'adin shekaru uku na shugabannin kananan hukumomi arba'in da hudu zai cika kuma yakamata a ce yanzu an kammala sabon zabe domin sabbin zababbun shugabannin su kama aiki daya ga wata mai zuwa amma kawo ya zuwa yanzu babu wani yunkuri ko tsare tsare da hukumar zabe mai zaman kanta take yi domin gudanar da sabon zabe.

Masu kula da alamura suna ganin wata dabara ce ta gwamnati domin gwamna ya samu damar nada kantomomin riko domin tafiyar da mulkin kananan hukumomin.

Alamarin yana tada hankulan masu ruwa da tsaki kan sha'ani dimukradiya musamman kungiyoyin dake rajin shugabanci nagari a dukanin matakai.

Kwamrede Nura Iro Ma'aji kusa a kungiyar C-Flak yace kawo yanzu a jihar Kano babu wanda zai ce ga wasu hujjoji a zahirance da zasu hana hukumar zabe da doka ta bata ikon gudanar da zabuka. Yace hakan yana nuna wa duniya irin mulkin kama karya da gwamnoni keyi a Najeriya. Gwamnonin na yin hakan ne domin su dinga yin yadda suka ga dama a jihohinsu. Inji Ma'aji idan ba'a yi hankali ba nan da kwana 22 sai a wayi gari a ji an nada kantomomi.

Dama an dade ana zargin gwamnoni da makure wuyan dimokradiyar Najeriya ta hanyar yin kememe wajen ba talakawa damar zaban wadanda zasu tafiyar da harkokin mulkin hukumominsu.

Kwamred Sa'idu Kabiru Dakata dan cibiyar Kitab mai rajin shgabanci nagari yace zasu cigaba da daukan matakan da suka dace cikinsu kuwa har da matakan shari'a domin ganin cewa gwamnatocin jihohi sun bi tanadin dokokin kasar dangane da lamuran da suka shafi kananan hukumomi.

Haka kuma ya kamata 'yan majalisu da suke da alhakin yin dokoki su sa kaimi domin a yi abun da yakamata saboda da zara wa'adin wadanda aka zaba ya cika ba'a yi zabe to an shiga hurumin doka. Su ma jam'iyyun siyasa kada su bar taronsu ya zama taron yuyuyu, inji Kabiru Dakata. Su ma yakamata su fara matsawa hukumar zabe lamba ta shirya zabe kan lokaci kamar yadda doka ta tanada.

Yanzu dai majalisar dokokin kasa ta kafa wata doka dake haramtawa gwamnoni nada kantomomi a kananan hukumomi.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Babu Alamar Za'a Yi Zaben Kananan Hukumomi a Kano - 3' 33"