Babu Isassun Matakan Kariya Daga Corona a Makarantu a Kebbi

Yayin da dalibai su ka koma makaranta da tsarin karatu kusan irin wanda aka saba da shi, masu lura da al'amura na ganin da alamar ba a dau ingantattun matakan kare dalibai ba a jahar Kebbi.

A jihar Kebbi da ke arewa maso yamamcin Najeriya, dalibai sun koma makarantu bayan da hukumomin kasar suka ba da umurnin a bude makarantu, sai dai masu lura da al'amura sun ce akwai rauni sosai dangane da matakan kare yara daga kamuwa daga cutar corona.

Dukkanin makarantun a jihar Kebbi sun bude kuma dalibai sun koma cike da shauki na komawa makaranta.

Gwamnatin jihar Kebbi ta amince cewa babu isassun matakan kariya daga cutar a makarantu amma akwai dabarun da ake yi. Kwamishinan ilimi a jihar Kebbi, Muhammadu Magawata Aliero ya ce gwamnatin ta na kokarin ganin an wadatar da kowane yaro da takunkumin rufe fuska.

Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Makarantun Kebbi Da Batun Corona