Babu Kwakwarar Shaida da Zata Sa A Gurfanar da Hillary Clinton A Kotu - FBI

Daraktan FBI James Comey

Hukumar dake binciken manyan laifuka a Amurka da aka sani da suna FBI ta bada umurnin kada a tuhumi Hillary Clinton tsohuwar sakatariar harkokin wajen Amurka, wadda ita ce zata zama 'yar takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar Democrat.

Hukumar ta binciki Hillary Clinton ne akan yin anfani da kafar karba da samun sako ta kanta ta yanar gizo wadda ake kira email maimakon ta yi anfani da na gwamnati. Hillary Clinton ta sha zargi daga jam'iyyar adawa ta Republican da ma wasu da suke yi mata kallon makaryaciya.

Wannan umurnin na FBI ya sauke mata wani kaya mai nauyi a yayinda take kokarin zuwa taron kolin jam'iyyarta cikin wannan watan inda za'a nadata a matsayin 'yar takara.

Hillary Clinton da James Comey

Daraktan hukumar FBI James Comey a lokacin da yake jawabi jiya Talata akan lamarin yi soki lamirin Hillary Clinton da ma'aikatanta yayinda take sakatariyar harkokin wajen Amurka daga shekarar 2009 zuwa 2013. Yace sun yi mugun sakaci yayinda suke aikawa juna sako ta email din da ita Clinton ta bude a gidanta dake New York.

James Comey yace amma duk binciken da suka yi suna duba dubban wasikun email basu ga wata shaida kwakwara ba da ta tuna Hillary Clinton ta yi abun da gangan ne ko domin son ranta da nufin karya dokar Amurka. Saboda haka babu wani mai gabatar da shari'a da zai iya gurfanar da ita da wata shaidar da zata sa kuliya ta hukumtata.

Tun farko dai sai da jami'an FBI suka kwashe sa'o'i uku da rabi suna yi mata tambaya a hedkwartarsu dake Washington DC, fadar gwamnatin Amurka.