Badakalar Daukan Ma’aikatan Lafiya A Jamhuriyar Nijar

Tambarin Jamhuriyar Nijar

A kasar jamhuriyar Nijar, kungiyar SYNAFPRA ta jami’ai a ofishin ministan kwadago ta bukaci hukumomin shara’ar kasar da su kara zurfafa bincike don gano masu hannu a zahiri cikin badakalar da tayi sanadiyar soke jarabawar samin aikin kiwon lafiyar al’uma 1800 a watan jiya har ma ta sa aka garkame wasu jami’ai a gidan yari.

A taron manema labarai da ya kira a ofishinsa lauyan gwamnati mai shigar da kara ya tabbatar da kaddamar da bincike kan wannan batu da yayi sanadiyar damke mutane 24 da ake zargi. Kafin daga bisani bincike ya bayar da damar sallamar wasu daga cikinsu, yayin da sauran kuwa aka tisa keyarsu zuwa gidan Yari.

Mai shari’a Mamman Tsayyabu Isah, yayi karin bayani kan wannan batu inda yace, sai da aka duba takardun sakamako har 28000, cikin su kuwa ansamu wasu da basu dauki jarabarba wasu kuma wadanda basu ci jarabawar ba amma an kara musu maki, wasu kuma an tauye musu hakki domin sunci jarabawar amma aka kayar da su.

Da jin wadannan bayanai kungiyar SYNAFPRA ta jami’an da wannan batu ya shafa, ta bukaci hukumomin shari’ar kasar Nijar da ta zurfafa bincike don gano zahirin masu hannu kan wannan harkalla.

Samun aikin gwamnati a jamhuriyar Nijar yanzu ya zama sai kana da hanya, lamarin kenan da yasa masu iko kasar suka soke jarabawa da yawa tsakanin wannan shekarar da wadda ta gabata.

Your browser doesn’t support HTML5

Badakalar Daukan Ma’aikatan Lafiya A Jamhuriyar Nijar - 2'38"