Bangaren Kungiyar Gwamnonin Nijeriya Na Zargin PDP Da Shishshigi

  • Ibrahim Garba

Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan

Mataimakin Shugaban bangaren Kungiyar Gwamnonin Nijeriya na zargin jam'iyyar PDP mai mulkin Nijeriya da yin katsalandan a zaben kungiyar na kwanan nan
Bangaren kungiyar Gwamnonin Nijeriya na zargin jam'iyyar PDP mai mulkin Nijeriya da shishshigi a zaben kungiyar na kwanan nan.

A hirarsu da wakilinmu na shiyyar Sakkwato, Murtala Faruk Sanyinna, Mataimakin Shugaban bangaren kungiyar Gwamna Abdul'aziz Yari Abubakar na jihar Zamfara ya ce dukkannin gwamnonin 35 sun kada kuri'unsu kuma gwamna Rotimi Amaechi na jihar Rivers mai samun goyon bayan mafiya yawan gwamnonin ya ci da kuri'u 19, yayin da shi kuma Gwamna Jonah Janga na jihar Filato mai samun goyon bayan jam'iyyar PDP ya sha kasa da kuri'u 16.

Gwamna Abubakar ya ce bangaren su gwamna Jang ba su ma da Sakatariya, kuma ba da dadewa ba gwamnonin za su hada kawunansu saboda kungiyar na da muhimmanci ga kowannensu.

Your browser doesn’t support HTML5

Bangaren Kungiyar Gwamnonin Nijeriya Na Zargin PDP Da Katsalandan - 2:19