An Nemi Theresa May Ta Sauya Yarjejeniyar Ficewar Birtaniya Daga Kungiyar Tarayyar Turai

A yau Wakilan tattaunawa na Birtaniya da Kungiyar Tarayyar Turai suka bayyana ra’ayoyi da suka ci karo da juna akan ficcewar Birtaniya daga Kungiyar Tarayyar Turai.

A yau Laraba Wakilan tattaunawa na Birtaniya da Kungiyar Tarayyar Turai suka bayyana ra’ayoyi da suka ci karo da juna akan ficcewar Birtaniya daga Kungiyar Tarayyar Turai, bayan da majalisar dokokin Birtaniya ta ba Fira minista Theresa May umarnin sauye yarjejeniyar ficcewar.

Wasu jerin kuri’un da aka kada a zauren Majalisar Birtaniya a jiya Talata sun amince da shirin jam’iyar May na neman wata yarjejeniyar.

A cikin wata hira a yau Laraba, Ministan Birtiniya mai kula da harkokin ficcewar Birtaniya daga Kungiyar Tarayyar Turai, Stephen Barclay ya fada wa kafar yada labarai ta BBC cewa sauye-sauye ne zai zama maudu’in tattaunawar da za a fara a ‘yan kwanaki masu zuwa.

Amma daga bangaren Kungiyar Tarayyar Turai, wakilin tattaunawar su Michel Barnier ya ce sun riga sun bayyana nasu ra’ayin