Boko Haram Damfara ce ba Addini Ba-Janar Buhari

Muhammadu Buhari, dan takarar shugabancin Najeriya a tutar APC.

Janar Muhammadu Buhari yace rikicin Boko Haram yana 'yan Najeriya akalla milyan biyu ayyukan yi.

Jiya Dantakarar shugabancin Najeriya a inuwar Jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari, ya gana da ‘yan kasuwa da masu masana’antu a jihar Kano kwana guda bayan yayi makamanciyar wannan ganawa da ‘yan kasuwar Jihar Lagos.

Da yake magana tunda farko Janar Buhari yayi alkawarin gwamnatin APC zata yi aiki tukuru wajen sake farfado da tattalin arzikin kasa, da ilmi da kuma noma.

Da yake magana kan tsaro, Janar Buhari yace kamin rikicin Boko Haram ta taso, akalla manyan motoci kusan dari suka zuwa arewa maso gabas. Kuma mutane akalla milyan biyu suke samun hanyoyin cin abinci.

Janar Buhari yace abunda Boko Haram take yi damfara ce, kuma ta'addanci ne, babu zancen addini cikin abunda suke yi. Daga nan yace duk gwamnati wacce take sahihiya zata dauki dukkan matakai na magance shi.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Janar Buhari ya gana da 'yan kasuwa a jihar kano da Legas