Boko Haram Sun Kai Hari a Garin Dapchi

Mayakan Boko Haram bangaren ISWAP sun kai hari a garin Dapchi, yayin da suka shiga dai-dai lokacin da mutanen garin ke shirye-shiryen buda baki suka yi ta harbe-harbe.

Wani mazaunin garin da abin ya faru a gabansa, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce bayan shigowarsu kai tsaye suka wuce cikin gidan hakimin garin, inda suka debi kayayyakin Abinci da sutura da ma sauran kayayyakin amfani sannan suka bankawa gidan wuta.

Shi ma daya daga cikin ‘ya’yan mai garin ya tabbatarwa da muryar Amurka faruwar lamarin, inda ya ce, mayakan sun kuma je karamin asibitin garin inda suka kwashe magunguna da dama, suka kuma bankawa Asibitin wuta.

Amma mazauna garin sun ce, sun ga isowar dakarun kasar da kuma jirgin yaki wanda ya tunkari ‘yan ta'addan tare da kone masu motoci biyu da ma halaka shida daga cikinsu.

Wani Hafsa a shelkwatar tsaron Najeriya ya ce, nan gaba kadan zasu fitar da sanarwa a hukumance mai cikakken bayani akan wannan hari na Dapchi.

Amma mai bincike kan kungiyar ta Boko Haram Dr. Kabiru Adamu ya ce, da ma akwai umarni da uwar kungiyar ISWAP ta duniya ta bayar kan kara zafafa hare-hare a kwanakin karshen na watan Azumin Ramadan, yana mai cewa ko bara warhaka an shaida irin yadda kungiyar ta yi ta kai irin wadannan hare-haren.

Saurari Karin bayani cikin sauti daga Hassan Maina Kaina.

Your browser doesn’t support HTML5

Mayakan Boko Haram Sun Kai Hari a Garin Dapchi