Boko Haram Ta Yi Garkuwa Da Mutum 14 a Kamaru

Sojojin Chadi na kare iyakar Najeriya da Kamaru.

Mayakan kungiyar Boko Haram sun yi awan gaba da mutane 14 a garin Kwalfata dake kusa da iyakar Kamaru da Najeriya.

Lamarin dai ya faru ne a wasu jerin hare-hare da mayakan Boko Haram ke kaiwa jihar Arewa Mai Nisa dake kasar Kamaru, inda a garin Kwalfata suka kama mutane 14 da suka hada da maza da mata, wadanda ya zuwa wannan lokaci babu wanda ya san inda suke.

Da yake yiwa Muryar Amurka karin bayani kan hare-haren, mazaunin yankin Alhaji Yaya Barista, ya ce karancin jami’an tsaro da sakaci a yankin sune ke haddasa karuwar hare-haren da ‘yan Boko Haram ke kaiwa.

Boko Haram dai na amfani da jiragen kwale-kwale a yankin biyo bayan toshe wasu hanyoyi da ruwa ya yi, lamarin da ya haifarwa jami’an tsaro tsaiko ga shiga yankunan domin bayar da kariya ga al’ummar.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Garba Awwal daga Kamaru.

Your browser doesn’t support HTML5

Boko Haram Ta Yi Garkuwa Da Mutane 14 a Garin Kwalfata - 2'57"