BRAZIL: An Ci Gaba Da Zanga-Zangar Neman Tsige Bolsonaro

  • Ibrahim Garba

Wasu masu zanga-zanga

Duk da killace kansa da Shugaban kasar Brazil ya yi saboda kamuwa da cutar corona, wannan bai sa masu zanga zangar kiran ya yi murabus tausaya masa ba.

Suna fushi ne saboda irin matakan da Shugaba Jair Bolsonaro ya dauka kan annobar, su ka yi ta ajiye gicciye a harabar ginin Majalisar Dokokin Tarayyar kasar a Brasilia, babban birnin kasar, don juyayin mutanen da cutar COVID-19 ta hallaka.

Shugaba Jair Bolsonaro

Masu zanga zangar, ciki har da mambobin kungiyoyin ma’aikata, da ‘yan asalin kasar, da kungiyar ‘yan luwadi da madigo, sun rubuta takardar hadin gwiwa ga Majalisar Dokokin kasar ta bukatar tsige Shugaban.

Bolsonaro ya sha suka saboda yadda ya yi ta shiriritar da barazanar annobar. Shugaban ‘yan asalin kasar, Kretan Kaingang ya ce wani dalilin zanga-zangar kuma shi ne karrama wadanda su ka rasa rayukansu sanadiyyar cutar corona.