Buhari, Atiku Sun Yi Allah Wadai Da Kisan ‘Yar Shugaban Afenifere

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari yayin ziyarar da ya kai Paris a watan Nuwamba 10, 2018.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi tir da kisan Mrs. Funke Olakunrin, diya ga shugaban kungiyar kare muradun Yarbawa ta Afenifere, Cif Reuben Fasoranti.

A jiya Juma’a ‘yan fashi suka harbe Funke har lahira akan hanyar Kajola-Ore a jihar Ondo da ke kudu maso yammacin Najeriya.

Wasu bayanai sun yi nuni da cewa mai rasuwar na kan hanyarta ta zuwa birnin Akure ne daga jihar Legas, a lokacin da 'yan bindigar suka budewa motar da take ciki wuta.

“Shugaban Muhammadu Buhari na mika sakon ta’aziyyarsa ga shugaban Afenifere, Pa Reuben Fasoranti, wanda ‘yan sanda jihar Ondo suka ce ‘yan fashi sun kashe diyarsa, Mrs. Funke Olakunrin akan hanyar Ondo-ore.” Wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaba Buhari, Femi Adesina, ya wallafa a shafinsa na Twitter ta bayyana.

Sanarwar ta kara da cewa, Shugaba Buhari ya kira “Pa Reuben Fasoranti ta wayar talho kan wannan abin alhini da ya samu diyarsa, ya kuma yi mai ta’aziyya tare da fatan Allah ya ba su hakurin wannan rashi.”

A Gaggauta Zakulo Wadanda Suka Kashe Funke – Atiku

Ana shi bangaren, dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar adawa PDP, Atiku Abubakar, ya yi kira ga jami’an tsaro da su hanzarta gudanar da bincike domin kamo wadanda suka aikata wannan kisa.

“Ina kira ga jami’an tsaro da su gaggauta kaddamar da bincike domin a kama wadanda suka aikata wannan kisa a kuma kawo karshen matsalar tsaron da ke addabar kasarmu.”

Atiku ya yi wannan kira ne a shafinsa na Twitter, inda ya kuma mika sakon taza’iyyarsa ga “Cif Reuben Fasoranti da iyalansa da kuma daukacin mambobin kungiyar Afinefere.”

Wasu rahotanni na zargin 'yan fashi da aikata wannan kisa, yayin da wasu ke nuni da cewa Fulani ne masu garkuwa da mutane.