Buhari Ya Tafi Portugal

Shugaba Buhari yayin wata tafiya da zai yi

Buhari ya kai ziyarar ce bisa gayyatar Shugaban kasar Portugal, Marcelo Rebelo de Sousa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya tafi kasar Portugal don gudanar da ziyarar aiki, wata sanarwa da kakakinsa Garba Shehu ya fitar ta ce.

Buhari ya kai ziyarar ce bisa gayyatar Shugaba Marcelo Rebelo de Sousa.

“Shugaban zai gana da takwaransa sannan za a karrama shi da lambar yabo mafi girma a kasar ta “Prince Henry.” In ji Shehu.

Ana sa ran shugabannin biyu za su tattauna kan batutuwan da suka shafi harkokin kasuwancin kasashen biyu, sannan za a rattaba hanu kan wasu yajeniyoyi.

Kazalika Buhari zai ziyaraci Majalisar Dokokin Portugal inda zai gana da shugabanta Dr. Agusto Santo Silva da kuma Firaminista kasar, Antonio Costa.

A gefe guda kuma shugaban na Najeriya har ila yau, zai halarci taron Majalisar Dinkin Duniya wanda ke tattaunawa kan kan tekunan duniya, wanda aka fara a ranar 27 ga watan Yuni.

A ranar Lahadi shugaban na Najeriya ya dawo daga Kigali, babban birnin Rwanda bayan da ya halarci wani taron koli na kungiyar kasashen da Ingila ta rena.

“A ranar Asabar, 2 ga watan Yuli Buhari zai koma Najeriya.” Sanarwar ta ce.