Burtaniya: Ana Nazarin Ingancin Maganin Flarin

A kasar Burtaniya, ana gudanar da bincike kan wani magani mai suna Flarin wajen tantance ingancinsa a illolin da cutar coronavirus ke janyowa a jikin dan adam.
Maganin wanda ake kuma kiran Lipid IBUPROFEN, yana iya kare cikin mutum daga abubuwa da dama.
Binciken mai taken Liberate Trial in COVID-19, yana da niyyar gwajin Flarin kan mutum 230 wadanda aka kwantar sakamakon covid 19, wadanda ke kuma ke fama da tsananin matsalar numfashi.
Amma mutanen da suka wuce shekara 18 ne kawai za a iya gudanar da gwajin kansu.
Majinyatan da jikinsu ya nuna bai iya daukar irin wannan maganin ko shiginsa, ba za a iya yin gwajin a kan su ba.