Canada Ta Kara Haraji Kan Kayan Amurka

shugaban Amurka Donald Trump da Firai Ministan Canada Justin Trudeau

Kasar Canada ta kara haraji kan kayan da kamfanonin Amurka ke sawarya a kasar, a wani mataki na maida martani kan karin harajin da Amurka tayi

Yau daya ga watan Yuli sabon harajin da kasar Canada ta sawa kayayyakin Amurka zai fara aiki, biyo bayan Karin harajin da shugaba Trump ya yi kan goran ruwa da karafan da kasar Canada ke sayarwa a Amurka.

Ofishin Firai minister Trudeau ya fada a wata rubutacciyar sanarwa cewa, Firai Ministan bashi da zabi, ya zama tilas ya sanar da daukar matakin maida martani kan Karin harajin da Amurka tayiwa goran ruwa da karafan, ranar daya ga watan Yuni ta wannan shekarar.

Ranar jumma’a Firai Ministan kasar Canada Justin Trudeau da shugaban Amurka Donald Trump suka tattauna kan harkokin cinikayya da tattalin arziki, bisa ga cewar fadar White House jiya asabar.

Tattaunawar da aka yi ta wayar tarho tsakanin shugabannin biyu ita ce ta farko tun bayan taron kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki G7. Bayan ganawar, Trump ya buga a shafinsa na Twitter cewa, Trudeau “bashi da karfin hali”, kuma “marar gaskiya”.

Kayan da ake sarrafawa a Amurka da Canada ta karawa haraji sun hada da markadadden tumatir da ake zubawa kan abinci, da injin yankar ciyawa da kuma kananan kwalekwale na nishadi masu gudun gaske a kan ruwa. Haka kuma giyar Whiskey na cikin jerin abinda kasar Canada ta karawa haraji. Ana sarrafa Whiskey ne a galibi a jihohin Tenessee da kuma Kentucky.