Chelsea da PSG, Real Madrid da Borussia Dortmund - 2/4/2014
WASHINGTON, DC —
Yau laraba ake ci gaba da gwabzawa a rana ta biyu ta zagayen farko na wasannin kwata fainal a gasar cin kofin zakarun kulob kulon na Turai.
A yau, Paris Saint Germain (PSG) zata karbi bakuncin Chelsea da manajanta Mourinho da karfe 8 saura kwata agogon Najeriya. A daidai wannan lokacin kuma, Real Madrid zata kece raini da Borussia Dortmund.
A jiya talata an tashi babu kare bin damo a dukkan wasanni biyun da aka yi, inda Manchester United ta yi 1-1 da Bayern Munich, yayin da su ma FC Barcelona da Atletico madrid suka tashi 1-1.
Za a yi karawa ta biyu tsakanin dukkan kungiyoyin a mako mai zuwa.
Your browser doesn’t support HTML5
Chelsea Zata Kara Da PSG, Yayin Da Real Madrid Zata Gwabza Da Borussia Dortmund - LARABA - 0'45"