Chelsea Ta Sayi Mykhailo Mudryk Daga Shakhtar Donetsk

Premier League - Mykhailo Mudryk

Ana fatan dan wasan zai taimakawa kungiyar ta Chelsea wacce ‘yan wasanta ke fama da rashin lafiya.

Kungiyar Chelsea ta gasar Premier League, ta sayo dan wasan Shakhtar Donetsk Mykhailo, duk da cewa, a ‘yan kwanakin da suka gabata, ana cewa dan wasa zai koma Arsenal ne.

Mudryk, wanda dan asalin Ukraine ne, ya rattaba hannun kan kwantiragin shekara takwas da rabi da kungiyar ta Chelsea.

“Wannan fitacciyar kungiya ce, a wata babbar gasa. Ina mai shaukin aiki tare da samun horo karkashin jagorancin Graham Potter.” Mudryk ya ce.

Dan shekaru 22, Mudryk, ya zura kwallaye goma a dukkan gasar da ya buga a wannan kaka.

Ana kuma fatan zai taimakawa kungiyar ta Chelsea wacce ‘yan wasanta ke fama da rashin lafiya.

Chelsea ta sha kaye a wasanni shida cikin tara da ta buga a wannan kakar wasa.

Bayanai sun yi nuni da cewa, tuni Mudryk ya isa Stamford Bridge akan kudi euro miliyan 70, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 62.

Dan wasan har ila yau zai rika karbar karin euro miliyan 30 (dala miliyan 27) a matsayin alawus-alawus.