Chen, Dan Gwagwarmaya Yana Son Barin China

A wan nan hoto lauya kuma dan gwagwarmaya Chen daga hanun dama, yana woya. Daga hanun hagu kuma jakadan Amurka a Beijing ne.

Dan gwagwarmayan nan makaho a China, wanda ya tsere daga daurin talala, kuma ya zauna na kusan mako daya a ofishin jakadancin Amurka a Beijing, ya bayyana burin barin kasar,

Dan gwagwarmayan nan makaho a China, wanda ya tsere daga daurin talala, kuma ya zauna na kusan mako daya a ofishin jakadancin Amurka a Beijing, ya bayyana burin barin kasar, sabo da yana fargba kan lafiyarsa data iyalinsa.

cya byar ofishin jakadancin Amurka jiya laraba, bayan da Amurka ta sami tabbaci da alkawarin daga jami’an kasar cewa, babu abinda zai taba lafiyarsa da ta iyalinsa, kuma za a kyaleshi ya ci gaba da karatunsa.

Chen ya gayawa manema labarai cewa, bayan ya sake hadewa da matarsa, sai ya fahimci irin barazanar da aka yi wa iyalinsa, daga nan ya fahimci cewa rayuwarsu tana cikin hadari.

Wani da ya kware kan harkokin China, Jerome Cohen, wanda har wayau abokin Chen ne, ya gayawa Muriyar Amurka cewa, bai san abinda Chen ya fadawa ‘yan jarida bayan ya bar ofishin jakadancin Amurka ba, amma a zantawa ta karshe da suka yi, Chen ya nuna dokin ci gaba da zama a China da shi da iyalinsa baki daya.