An zakulo Fiyeda Ma'aikatan Hakar ma'adinai Ashirin Da Hudu Da Suka Makale Karkashin Kasa Fiyeda Wata Biyu

Masu aikin ceto a kasar Chile suke zura gugar da ake amfani da ita wajen zakulo ma'aikata da suka makale.

Ministan hakar ma'adinai na kasar Chile yace zuwa daren yau agogon kasar,za'a kammala zakulo dukkan ma'aikatan d a suka makale tun farkon watan Agusta,lokacin kasa ya burma rami da suke aiki ciki.

Daya bayan daya masu aikin ceto na zakulo mahaka ma’adinan talatin da uku yan kasar Chile, wadanda tun farko watan augusta suka makale a karkashin kasa.

Ya zuwa yanzu da muke baku wannan labari an ceci mahaka ma’adinai ashirin da hudu a aikin ceton mai sarkakiya da ba kasafai ake fuskantar irinsa ba. Ana fiddo wadannan mahakan ta wani abu mai kama da guga, a yayinda iyalansu da jami’ai suke jira.

Wasu da aka zakulo su,sai su durkusa su yiwa Allah godiya kafin a kaisu asibiti domin binciken lafiyarsu. Wadannan mahakan ma’adinai sunyi kwanaki sittin da tara a makale a karkashin kasa.

Ministan kiwon lafiya na Chile, Jaime Manalich yace wadanda aka ceta ya zuwa yanzu lafiyarsu kalau. Bayan da aka ceci mahaki na farko, shugaban kasar Chile Sebastian Pinera, ya fadawa manema labaru cewa ceton mahakan ma’adinai talatin da uku ne abinda gwamnatinsa tafi maida hankali akai cikin watani biyu da suka shige.

Shugaba Pinera yace dama sai da gwamnatinsa ta lashi takobin cewa sai ta nemo mahaka ma’adinai har ta gano su, sai gashi Allah ya basu ikon cika wannan alkawari za’a zakulo su a maida su gidajensu lafiya.