Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ceto Dukkan Mahaka Ma'adinai 33 Daga Karkashin Kasa A Chile


An Ceto Dukkan Mahaka Ma'adinai 33 Daga Karkashin Kasa A Chile

A karon farko cikin makonni 10, mahakan sun ga iyalansu da kuma hasken rana bayan da aka samu nasara ciro su cikin wata guga ta musamman mai kama da sunduki.

Dukkan mahaka ma’adinai 33 wadanda suka shafe fiye da watanni biyu cikin ramin hakar ma’adinai mai zurfin fiye da rabin kilomita sun sanya idanu kan iyalansu a bayan da aka samu nasarar ceto su daga wannan ramin.

An zakulo mahakan daya bayan daya cikin wata guga ta musamman mai kama da sunduki, inda suka sumbanci iyalansu da kuma shugaba Sebastian Pinera na kasar ta Chile. A bayan da aka zakulo wani mai suna Victor Zamora, shugaba Pinera ya fada masa cewa ba shi kadai ya ji jiki ba, yana mai fadin cewa gwamnati ta cika alkawarin da ta yi na zakulo mahakan da ransu.

Mutumi na karshe da aka zakulo daga cikin ma’aikatan shi ne Luis Urzua, Foman na wadannan ma’aikata a ranar 5 ga watan Agusta, ranar da bakin ramin hakar ma’adinan ya rusa ya toshe su a karkashin kasa. Ana yaba ma Urzua a zaman mutumin da ya samu nasarar kwantar da hankulan wadannan mahaka a yayin da masu aikin ceto a kan doron kasa suke ta kokarin neman sanin ko mutanen su na da rai tare da kokarin samo hanyar da za a bi wajen fito da su a bayan da aka gano su na da rai.

An Ceto Dukkan Mahaka Ma'adinai 33 Daga Karkashin Kasa A Chile
An Ceto Dukkan Mahaka Ma'adinai 33 Daga Karkashin Kasa A Chile

Mutum na karshe daga cikin ma’aikatan ceto 6 da aka zura cikin ramin domin taimakawa wajen fito da wadannan ma’aikata shi ma ya komo kan doron kasa jim kadan bayan karfe 12 na dare agogon Chile, sa’o’i 24 a bayan da mutum na farko da aka ceto ya iso kan doron kasa.

Wannan aikin ceto mahakan daga karkashin kasa ya dauke hankulan al’ummar Chile da miliyoyin mutane a fadin duniya, wadanda suka yi tsaye cik su na kallon ikon Allah a yayin da mahakan dake fitowa su na rungumar iyalansu bayan da suka shafe makonni 10 cikin ukuba a karkashin kasa. Wasu daga cikin mahakan sun durkusa su na addu’ar godiya ga Ubangiji kafin a dauke su zuwa asibiti inda za a duba su na tsawon kwanaki biyu kafin kowannensu ya koma gida.

XS
SM
MD
LG