Coronavirus: An Dage Gasar Kwallon Kwando Ta Afirka

'Yan wasan kwallon kwando a Somalia

Yayin da ake fargabar yaduwar cutar coronavirus, hukumar gasar kwallon kwando ta Afirka, za ta dage wasannin farko da za a fara a wannan wata, a cewar shugaban gasar Amadou Galo Fall.

“Mun yanke shawara mu jinkirta wasannin, muna kuma shirin fara wa nan gaba a cikin wannan shekara da zaran al’amura sun daidaita.” Fall ya fada wa Muryar Amurka.

Ita dai wannan sabuwar gasa ta hadin gwiwa ce tsakanin hukumar kwallon kwando ta duniya NBA da takwararta ta Afirka.

An kuma tsara za a kaddamar da ita a wannan wata ne inda kungiyoyi 12 daga sassan Afrika za su kara.

Hakan na faruwa yayin da rahotanni ke nuna cewa, hukumar kwallon kwando ta Amurka NBA, ita ma ta aika wa da kungiyoyin gasar da su zauna da shirin kara wa ba tare da ‘yan kallo a fili ba, gudun kada a yada cutar.

Hukumomi da kasashe da dama na ta daukan matakan dakile yaduwar cutar ta coronavirus wacce ta faro daga China.

Ya zuwa yanzu ta kama kusan mutum 100,000 a duk fadin duniya, yayin da wasu dubbai suka mutu.