Coronavirus Ka Iya Tasiri a Afirka Saboda Matsalolin Fannin Kiwon Lafiya

Afirka ta zamanto nahiyar da take da karancin masu fama da matsalar cutar coronavirus, inda adadin mutanen da suka kamu da ita bai wuce daruruwa ba idan aka yi la'akkari da jimullar mutum dubu 200 da suka kamu da cutar a duniya.

Amma jami'an lafiya na fargabar cewa, annobar ka iya yin mummunan tasiri a nahiyar, lura da dumbin matsalolin da fannin kiwon lafiyar nahiyar ke fuskanta.

Sannu a hankali, kasashe akalla 30 ne aka samu bullar cutar, wadanda suka hada da Burkina Faso, Kamaru, Habasha, Najeriya, da Kuma Segenal wadanda ke da adadi mafi yawa a yankin kasashen da ke kudu da Sahara.

To amma duk da cewa nahiyar ita ke da adadi mafi karanci idan aka kwatanta da sauran sassan duniyar da aka samu bullar cutar, Shugaban hukumar lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Gebereyesus, ya ce akwai bukatar hukumomi a nahiyar su yi tukin-tsaye wajen ganin sun dauki matakan dakile bazuwar cutar.

Jami'an lafiya a nahiyar dai sun fi nuna damuwa ne kan yadda yaduwar cutar ta coronavirus ka iya dagula al'amura a nahiyar, wacce wasu sassanta ke fama da dumbin matsaloli na cututtuka.​