Coronavirus Ta Kashe Mutum Na Farko a Wajen China

Wasu 'yan kasar Philippines sanye da makarin baki a yau Lahadi domin kare kansu daga cutar Coronavirus, Fabrairu. 2, 2020.

A yau lahadi, cutar Coronavirus mai saurin kisai, ta halaka mutum na farko a wajen kasar China inda cutar ta samo asali.

Lamarin ya faru ne a kasar Philippines.

Jami’an kiwon lafiya a tsakiyar Lardin Hubei, inda cutar ta barke, sun ce mutum 304 ne suka mutu ya zuwa yanzu a China, sannan wasu dubu 14 suke dauke da ita.

Tun a makonnin da suka gabata aka garkame birnin Wuhan a lardin Hubei, amma jami’ai har ila yau sun ce an rufe birnin Wenzhou ma a yau Lahadi.

Wenzhua na da tazarar kilomita 800 tsakaninsa da Wuhan.

Rahotanni sun nuna cewa wasu mazauna birnin na Wuhan sun yi zargin cewa an yi rufa-rufa tun farkon bullar cutar, ciki har da mazauna yankin da likitoci.

Bayanai sun yi nuni da cewa, yin magana kan cutar wacce ta bulla a watan Disamba, kan sa jami’an gwamnati su yi wa mutum barazana a wasu lokuta ma har da tsarewa.

“Tuni rade-radin wannan lamari ya fantsama a shafukan intanet,” in ji Flora Fauna, Ba’amukiya ‘yar asalin yankin Wuhan wacce ta boye sunanta yayin wata ganawa da ta yi da Sashen Mandarin na VOA.

“Maimakon a dauki matakan da suka dace, sai gwamnatin birnin ta turo ‘yan sanda suna kama mutanen da ke yada labaran,” a cewar Fauna.