Coronavirus: Trump Ya Kwantar da Hankalin Al'umma Dangane Da Batun Abinci

Shugaban Amurka Donald Trump da wasu jami’an gwamnatin kasar, suna kokarin kwantar da hankalin jama’a a kasar, bayan da kantuna da dama suka kasance fayau, sakamakon saye kayan da mutane suka yi don shirin ko-ta-kwana saboda cutar coronavirus.

Bayan ganawarsa da shugabanin manyan shaguna 30 na kayan abinci, shugaba Trump ya ce “mutane ba su bukatar sayen kayan abinci da yawa, ya kamata su kwantar da hankalinsu.”

Donald Trump ya kara da cewa “ba bu karancin abinci a kasar, illa dai kawai mutane ne ke linka abubuwan da suke saye sau ukku ko biyar fiye da abinda suke bukata.