Gwamnati Ta Katse Hanyoyin Sadarwa a Habasha

Wata waya a hannun wani

An katse wa dubban ‘yan kasar Habasha da ke yammacin Oromia hanyoyin sadarwar waya da yanar gizo, saboda dakatar da harkoki da gwamnati ta yi.

Kungiyar da ke sa ido kan take hakkin bil Adama ta HRW ce ta bayyana hakan.

"Shi kansa rashin samun bayanan wani babban al'amari ne, saboda ‘yan Habasha na bukatar bayanai kan yadda cutar Coronavirus ke yaduwa a fadin duniya," a cewar kungiyar.

Haka kuma dakatar da harkokin da aka yi, ya sa ya na da wahala ga masu saka ido daga waje su auna abin da mutane suke bukata na jin kai a yankin Oromia.