COVID-19: Ana Sa Ran Sakin Tsohon Lauyan Shugaban Amurka

Ana sa ran sakin tsohon lauyan Shugaban Amurka Donald Trump daga gidan yari nan ba da jimawa ba, a dalilin samun barkewar annobar COVID-19 a gidan yarin da yake kulle.

Michael Cohen, wanda aka yanke wa zaman gidan kaso na tsawon shekara uku, an shirya sakin shi daga gidan yari na Otisville dake birnin New York a karshen shekara mai zuwa.

Zai karkare sauran lokacin nasa ne yana daurin talala a gidansa.

A shekarar 2018 Cohen ya amince da aikata laifin yin coge a wajen biyan kudaden haraji, da zarmiya da kudaden yakin neman zabe, da kuma yi wa majalisa karya.

Cohen kuma ya amince da laifin bai wa wasu ‘yan mata biyu kudade na toshiyar baki wadanda suka ce suna da wata alaka da Shugaba Donald Trump, lamarin da Shugaba ya karyata.

Za a killace Cohen tsawon kwanaki 14 a gidan yarin kamin a sake shi.