COVID-19: Halin Da Ake Ciki a Wasu Kasashen Duniya

A yau Laraba kasar Spain ta sanar da cewa adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu ta cutar coronavirus ya zarta 100,000 a kasar, yayin da wani babban jami’in kasar Saudiyya ya bukaci mutanen da suke da niyar zuwa aikin hajji da su dan dakata da yanke shawara a yanzu.

Spain tana daya daga cikin wuraren da cutar ta fi kamari a duniya, inda take bin bayan kasashen Amurka da Italiya a yawan wadanda suka kamu da cutar. Sanarwar ta yau Laraba ta kuma hada da adadin wadanda suka mutu zuwa yanzu da ya haura sama da 9,000.

Musulmai na shirin tafiya Saudiyya aikin Hajji daga dukkan kasashen duniya a karshen watan Yuli a zaman daya daga cikin rukunan addinin. Amma saboda yaduwar wannan kwayar cuta, da kuma hana shiga biranan Makka da Madina da Saudiyya ta yi, Mininstan da ke kula da aikin Hajji da Umrah na saudiyya Muhammad Saleh bin Taher Banten, ya fada wa gidan talabijin na kasar cewa mutane su dan jinkirta tukunna, kafin kasar ta yi karin haske a kan irin halin da ake ciki.

A Amurka kuwa, jami’ai sun yi hasashen yuwuwar mutuwar mutane 100,000 zuwa 240,000 sakamakon cutar coronavirus, yayin da suke kara jaddada bukatar a ci gaba da aiki da matakan ba juna tazara don a samu a rage adadin hasashen.

Dr. Anthony Fauci, daraktan cibiyar da ke kula cututtuka masu yaduwa, ya ce yana fatan adadin ba zai kai haka ba, amma gaskiyar ita ce mutane su shirya.