COVID-19: Kungiyoyin Makiyaya Sun Koka A Jamhuriyyar Nijer

Kasuwar dabbobi a jamhuriyar Nijar

A jamhuriyar Nijer kungiyoyin makiyaya sun koka a game da faduwar dajarar dabobi a kasuwanni sanadiyar anobar cutar coronavirus.

Kusan ana iya cewa harkoki sun tsaya cik a kasuwannin dabobi a yankunan arewacin jihohin Maradi, Tahoua, Agadez da Tilabery, lamarin da ya zama barazana ga mazauna karkara musamman wadanda ke dogaro da kiwon dabobi wajen daukar dawainiyar iyali, a saboda haka suka bukaci hukumomi su dubi wannan matsala da suka shiga.

Shugabannin kungiyoyin makiyaya sun alakanta matsalar da matakan da gwamnatin Nijer ta dauka da nufin dakile yaduwar cutar COVID-19.

Shugaban kungiyar da ake kira JINGO ya ce makiyaya sun dogara da sana’ar sayar da dabbobi, amma yanayin da ake ciki ya sa basa iya sayar da dabbobin.

Altine Hassan ya ce Halin da ake ciki a yau ya fara haddasa zaman zullumi a bangaren Fulani makiyaya a karkara.

Shugaban kungiyar CAPAN Sanda Banmi, ya ce Irin wannan yanayin ya fi shafar galibin yankunan da kiwo ke matsayin aikin da jama’arsu ke dogaro da shi.

Yanzu dai hankalin kungiyoyin Fulani makiyaya ya karkata wajen hukumomi, domin suna sa ran samun mafitar wannan matsala.

Kungiyoyin makiyayan sun kara da cewa matakin rufe iyakokin kasashe sanadiyyar annobar coronavirus ya rutsa da wasu Fulani ‘yan Nijer dake cirani a kasashen Mali da Burkina Faso saboda haka suka yi kira da a gaggauta daukar matakan maido su cikin dangin su.

Saurari karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

COVID-19: Kungiyoyin Makiyaya Sun Koka A Jamhuriyyar Nijer