COVID-19: Mabambantan Ra'ayoyi Kan Kasuwannin Wucin Gadi a Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta amince da kafa kasuwannin wucin gadi a makarantun firamare na gwamnati don dakile yaduwar cutar coronavirus biyo bayan rufe kasuwannin jihar. A ranakun Laraba da Asabar kasuwannin na wucin gadi zasu yi aiki don ba jama’a damar fita neman abinci.

Ranar Laraba 6 ga watan Mayu ne gwamnatin jihar ta fara aiwatar da tsarin bayan rufe dukkan hanyoyin da ke kusa da manyan kasuwannin birnin Kaduna, abinda ya janyo cunkoso da doguwar tafiya da kafa ga mutanen da ke son zuwa wuraren da ke dab da kasuwannin. Jami'an tsaro sun yi ta sintiri suna korar 'yan kasuwa da wadanda suka je cin kasuwa a kwaryar birnin Kaduna .

Wasu ‘yan jihar sun bayyana mabambantan ra’ayoyi a game da matakin wanda wasu ke gani cunkoson da ake samu yanzu sakamakon sabon tsarin kadai ya isa ya kara baza cutar yayin da wasu kuma ke gani matakin ya yi daidai.

Idrissu Alami, na daga cikin wadanda ke kallon tsarin a matsayin na takura duba da cewa lokacin damina ne yanzu ga shi babu rumfuna a makarantun kuma 'yan kasuwa na nuna damuwa kan baje kayayyakinsu saboda yanayin tsaro.

“Dole ce ta sa gwamnatin jihar daukar wannan matakin saboda larurar da ake fuskanta ta annobar cutar coronavirus,” a cewar malam Abdallah Yunus Abdallah, mai taimaka wa gwamnan jihar kan kafafen yada labarai. Ya kuma yi kira ga al’umma da su yi hakuri da yanayin da ake ciki saboda gwamnatin jihar na bin shawarwarin kwararru ne.

Saurari karin bayani cikin sauti daga Isah Lawal Ikara.

Your browser doesn’t support HTML5

COVID-19: Mabambantan Ra'ayoyi Kan Kasuwannin Wucin Gadi a Kaduna