COVID-19: New Zealand Da Thailand Na Kokarin Kara Sassauta Dokar Zirga-zirga

Kasashen New Zealand da Thailand sun bayyana cewa a jiya Talata ba wanda ya kamu da cutar coronavirus a cikin kwana daya, hakan na zuwa ne a yayin da kasashen biyu ke kokarin kara sassauta dokokin takaita zirga-zirga sakamakon cutar coronavirus.
New Zealand dai ta samu kwannaki hudu da ba wanda ya kamu da wannan cutar duk a cikin makon nan, lamarin da ya kara nuna alamun nasarar dokar kullen da aka yi fama da ita na wata daya a kasar.

A yau ne yawancin shaguna da gidajen cin abinci zasu bude a kasar, amma dukkaninsu zasu yi amfani da dokar bada tazara.

A cewar darakta janar na kiwon lafiya a kasar Ashley bloomfield, “Mutane sun kagara a bude wurare, kuma hakan bai zo da mamaki ba.”