COVID-19: 'Yan Ci Rani Na Fuskantar Rashin Tabbas A Thailand

  • Ibrahim Garba

Wasu 'yan ci rani a kasar Thailand

Ma’aikata ‘yan cirani da su ka makale a Thailand tun bayan kafa dokar takaita zirga-zirga a watan Maris, na fuskanta makoma marar tabbas da kuma tsadar rayuwa, duk kuwa da tallafin da gwamnatin kasar ke bai wa leburori marasa ayyukan yi a kasar.

‘Yan kwanaki kawai bayan kafa dokar bayar da tallafin gaggawa ranar 23 ga watan Maris, kasar Thailand ta yi shelar rufe dukkan iyakokinta, ta kuma yi shelar shirin bayar da tallafi ga ma’aikatan da dokar takaita zirga-zirgar ta shafa – walau ‘yan asalin Thailand din ko baki.

To amma sharuddan samun tallafin sun hada da mallakar asusun banki, da kuma shaidar an bayar da gudunmowa ga gidauniyar gwamnati na tsawon akalla wata shida, wanda hakan ya kai ga ware mafiya talauci, ciki har da miliyoyin ‘yan cirani da su ka zo daga kasashe makwabta.