COVID-19: ‘Yan Sanda Sun Cafke Mutane 300 a Jamhuriyar Nijer

A jamhuriyyar Nijer hukumar ‘yan sanda ta bada sanarwar cafke mutane kusan 300 daga ranar 17 zuwa 21 ga watan nan na Afrilu a birnin Yamai inda aka fuskanci jerin zanga-zangar matasa sakamakon kosawa da dokar hana fitar dare da hana sallar jam’i da Juma’a, a matsayin wani bangare na matakan da hukumomi suka dauka da nufin dakile yaduwar cutar coronavirus.

A wata sanarwa da daraktan yada labarai a hukumar ‘yan sanda ta kasa kwamishina Aboun Moutari ya sanya wa hannu, hukumar ta ‘yan sanda ta yi wa jama’a bayani dangane da abubuwan da suka faru a daren ranakun 17,18 da 19 na watan Afrilu da wadanda suka wakana a daren 21 a birnin Yamai inda aka fuskanci tarzomar matasa.

Hukumar ‘yan sandan ta ce mutunta ka’idodin da gwamnati ta shimfida da nufin dakile yaduwar cutar COVID-19 ya zama wajibi saboda haka ta bukaci hadin kan jama’a don ganin an samu nasarar abinda aka sa gaba.

A karshen watan Maris da ya gabata ne shugaba Issouhou Mahamadou ya kafa dokar hana fita daga karfe 7 na yamma zuwa 6 na safe a Yamai, tare da killace birnin daga sauran sassan kasar 'yan kwanaki bayan da aka gano mutun na farko da ya harbu da kwayar cutar coronavirus a Nijer, matakin da wasu ‘yan kasa ke fatan ganin an sassauta ko kuma an cire shi kwata-kwata domin jama’a su sami damar morar ‘yancin walwala.

Saurari karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

COVID-19: ‘Yan Sanda Sun Cafke Mutane 300 a Jamhuriyyar Nijer