Cutar Coronavirus Na Saurin Yaduwa, a Yi Hattara - Mohammed Atiku

Mohammed Atiku Abubakar, dan tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar.

Yayin da adadin wadanda suka warke daga cutar coronavirus a Najeriya ya haura 300, Mohammad Atiku Abubakar, dan tsohon mataimakin Shugaban kasar Najeriya Atiku Abubakar na daya daga cikin wadanda suka kamu da cutar amma suka warke.

A wata hira da Muryar Amurka, Mohammed ya fadi cewa takamaimai ba zai iya cewa ga inda ya kamu da cutar ta coronavirus ba amma dai ya san a kasar waje ya dauko ta kafin ya dawo Najeriya. Ya ce bai ji dadi ba kuma ya kasance a cikin yanayin fargaba saboda yana daga cikin mutanen farko da suka kamu da cutar a Abuja.

Alamomin cutar coronavirus dai sun hada da masassara mai zafi, tari da matsalar numfashi, amma Mohammed ya ce tun daga lokacin da aka tabbatar ya kamu da cutar zuwa lokacin da aka sallame shi daga asibiti babu wasu alamomin cutar a tattare da shi.

Duk da cewa wasu kwararru, har ma da shugaban Amurka Donald Trump sun ce za a iya amfani da maganin Chloroquine na jinyar masassarar cizon sauro wajen jinyar coronavirus, Mohammed ya ce a iya saninsa ya zuwa yanzu babu maganin cutar.

Mohammed ya kuma ce babu ko sisi da ya kashe a lokacin da ya ke killace a asibiti tsawon kwana 40 saboda gwamnati ce ke daukar nauyin jinyar masu cutar. Ya kuma ja hankalin jama’a akan su kula sosai don cutar na saurin yaduwa. Idan mutum daya ya kamu da cutar a gida, to idan ba a yi hankali ba sai duk mutanen gidan sun kama inji shi.

Saurari cikakkiyar hirar Muhammed da Madina Maishanu.

Your browser doesn’t support HTML5

Cutar Coronavirus Na Saurin Yaduwa a Yi Hattara – Muhammed Atiku