Cutar COVID-19 Na Ci Gaba Da Bazuwa a Wasu Jihohin Amurka

Adadin masu kamuwa da cutar coronavirus ya zarta miliyan 11 a fadin duniya, yayin da cutar ke ci gaba da bazuwa a kasashe da yawa ciki har da Amurka, inda alkaluma suka nuna mutum 57,000 suka kamu da cutar a rana guda, wannan shine adadi mafi yawa da aka samu a kasar.

Jihar Florida ta sanar da samun mutum 9,488 da suka kamu da cutar a ranar Juma’a 3 ga watan Yuli, kwana daya bayan da jihar ta samu adadi mafi yawa a rana guda na sama da mutum 10,000 da suka kamu da cutar.

Jihar Florida

Hukumomin jihar Florida sun ce bangaren jinyar marasa lafiya na musamman a asibitocin jihar ya cika da kusan kashi 80 cikin 100, yayin da a jihar Arizona kuma kashi 91 cikin 100.