Cutar Ebola Ta Halaka Mutum 2,218

WHO - World Health Organization

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce rashin tsaro da kuma rashin iya kai wa ga wasu yankunan Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, su ne manyan matsalolin da ke kara kawo cikas ga yunkurin dakile cutar Ebola a kasar.

Alkaluman da aka samu a baya-bayan nan a kasar sun nuna cewa mutum 3,354 ne suka kamu da cutar, yayin da mutum 2,218 suka rasa rayukansu.

Cutar Ebola

Jami’an lafiya dai na ta kara damuwa ganin cewa hannun agogo na iya komawa baya game da ci gaban da aka samu wajen dakile cutar ta Ebola a yankunan Kivu ta Arewa da Ituri saboda ci gaba da fada da ake yi tsakanin kungiyoyin mayaka da dama.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce an kawar da wannan mummunar cutar daga yankuna 25 da ke fama da ita.

Daraktan shirin dakile cututtuka na WHO Michael Ryan, ya ce “abin mamaki ne yawan karuwar da ake ta kara samu a yankin Arewacin Kivu, a cikin makon da ya gabata kawai, mutum 27 sun kamu da cutar".