Cutar Ebola Ta Sake Bullowa

Ma'aikatan kiwon lafiya na ebola

Yayinda aka yi makonni ba'a samu sabon kamu da ebola ba sai kwatsam gashi cutar ta sake kunno kai

A karon farko cikin wannan shekarar an samu karuwar wadanda suka kamu da cutar ebola a kasashen yammacin Afirka uku inda har yanzu ake fama da cutar.

Hukumar kiwon lafiya ta duniya ko WHO a takaice tace an samu mutane 124 da suka kamu da cutar a karshen makon jiya.

Kasar Saliyo ce take kan gaba inda mutane 80 suka kamu. Sai kasar Guinea inda aka samu 39. A Liberiya kuwa an samu mutane biyar.

A wani sabon rahoto da hukumar kiwon lafiya din ta fitar jiya Laraba tace akwai bukatar a gaggauta a shawo kan sabuwar barkewar kafin damina ta kankama lokacin da shiga kauyuka zai yi wuya.

Tun lokacin da annobar ta barke mutane kusan 22,500 suka kamu da cutar a kasashe uku kuma adadin wadanda suka mutu ya dara 9,000.

Cutar tayi kamar ta tsaya domin an samu makonni da dama babu sabbin kamu.

Dama kwararru a kiwon lafiya sun yiwa yankin yammacin Afirka din kashedi cewa kada su saki jiki domin cutar ka iya dawowa.

Hukumar kiwon lafiya ta duniya tace jana’izar da aka yi a yankin Lola a kasar Guinea watan jiya ba bisa bin ka’idodin da ta tsara ba yayi sababin da mutane 11 suka kamu da cutar.

Wajibi ne a bi ka’idodin binne gawa domin mutane na iya kamuwa da cutar idan itace tayi sanadiyar mutuwar.

Ranar Litinin din nan aka fara gwajin allurar rigakafin cutar a kasar Liberia.