Cutar Ebola Zata Durkusar da Tattalin Arzikin Saliyo , Liberiya da Guinea

Ebola a Saliyo

Kwararru daga hukumar bada lamuni ta duniya da bankin duniya suna harsashen cutar ebola zata yiwa tattalin arzikin kasashen Saliyo, Liberiya da Guinea muguwar illa

Kwararru daga hukumar bada lamuni ta duniya ko IMF da bankin duniya sun ce ebola na raunata tattalin arzikin kasashen Saliyo , Liberiya da Guinea.

Kusan kimanin mutane 3,500 cutar ta kashe kana kuma akwai dubun dubatan mutane da suka kamu da cutar a kasashen.

Hukumar bada lamuni ta duniya tace ebola tana durkushe tattalin arzikin wasu yankunan Afirka ta Yamma. Wannan harsashen ya fito ne jiya Talata bayan da hukumar ta buga wani nazari da tayi akan tattalin arzikin kasashen dake kudancin hamadar Afirka. Nazarin ya nuna cewa tattalin arzikin kasashen Afirka kusan goma sha biyu zai bunkasa da kashi 5.8 shekara mai zuwa.

Jami’an bankin duniya sunce idan ba jajircewa aka yi ba a dakile cutar tana iya kawo cikas a harkokin kasuwanci da yawon bude ido da tafiye- tafiye.