Da Batun Tsaron Najeriya Na Ke Kwana Na Tashi – Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya ce yana daya daga cikin shugabannin kasashen duniya da suke fama da rashin farin ciki a dunya.

Buhari na magana ne kan yawan hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da suka addabi wasu yankunan kasar, kamar yadda wata sanarwa dauke da sa hannun kakakinsa Malam Garba Shehu ta nuna, wacce Muryar Amurka ta samu.

“Ta yaya zan zama mai farin ciki da nuna halin ko-in-kula yayin da ‘yan bindiga ke kashe ‘yan Najeriya? Ni mutum ne, kuma na san zafin da wadanda abin ya shafa da iyalansu suke ji, wadanda aka jefa cikin halin kunci sanadiyar neman kudaden fansa da ‘yan bindiga ke yi daga gares su.” Sanarwa ta bayyana.

Shugaban na Najeriya, ya sha suka a ‘yan kwanakin nan, saboda hare-haren da ake kai wa a Zamfara, wadanda suka ki ci suka ki cinyewa.

Dadin dadawa, shugaba Buhari ya kuma fuskanci suka, bayan da aka zarge shi da yin jaje kan kisan wani matashi a kudancin kasar, ba tare da ya yi hakan ba kan kisan da ya faru a Zamfara a baya-baya nan, inda dumbin mutane suka mutu.

A karshen makon nan, an gudanar da zanga zanga a wasu sassan arewacin Najeriya domin jan hankalin gwamnati ta dauki mataki kan wadannan kashe-kashe.

Sai dai sanawar ta bayyana Buhari yana cewa, “yadda ake saka siyasa a cikin irin wannan mummunan yanayi, ya nuna yadda siyasarmu take cikin hali na rashin ci gaba. A kowane mako, na kan gayyaci hafsoshin tsaro, domin su yi min bayani kan irin dabarun da suke amfani da su domin samun galaba akan wadannan masu kisa.”

Buhari ya kara da cewa, “babu wani batu da na ke kwana na tashi da shi kamar batun tsaro. A matsayi na shugaban kasa, kare rayukan 'yan Najeriya na daga cikin abubuwan da gwamnatina ta sa a gaba.”