Da Dan Gari: Tarihin Garin Getso, Jihar Kano

A wannan makon gidan rediyon jihar Kano a Najeriya ya kai ziyara garin Getso da ke karamar hukumar Gwarzo a jihar Kano don jin tarihin garin.

Garin Getso da ke yammacin birinin Kano, ana yi masa kirari da "Getso marayar Gwarzo" kuma ya wanzu ne tun lokacin maguzawa a wajajen shekarar dubu da dari biyar, daga bisani hausawa Babe suka karbi ragamar ikonsa sannan a lokacin jihadin Shehu Usman Dan fodiyo a shekarar dubu da dari takwas da hudu, Fulani makiyaya daga kasar Sokoto suka karbe ragamar mulkinsa.

Muhammadu Bello, Dagacin garin na goma sha shida a jerin Fulani, ya fadi cewa sana'ar dinki na daga cikin sana'o'in da aka san 'yan garin da ita.

Saurari cikakken shirin wanda Adamu Ibrahim Dabo ya gabatar:

Your browser doesn’t support HTML5

Da Dan Gari: Tarihin Garin Getso, Jihar Kano