Abdul'azeez Idi Kotoko na Alpha Rediyo Kumasi, ya yi hira da sarkin Zangon Atibobo mai Martaba Ufailu Dan Usman don jin dan takaitaccen tarihin Zangon.
WASHINGTON, D.C —
Zangon Atibobo tsohon gari ne wanda ya shahara a matsayin Zango mafi girma a Ghana saboda a baya, wuri ne da ake cinikin bayi. Hausawa ne ke zama a garin, a cewar Ufailu.
Basaraken ya ce babban kalubalen da suke fuskanta shine yadda ake yi musu kallon baki, duk da cewa kakannin kakanninsu a Ghana aka haifesu, bayan haka suna fuskantar rashin ruwa.