Da Dan Gari: Tattaunawa Da Sarkin Zango

Gidan rediyon Alpha na garin Kumasi ya yi hira da sarkin Zango na jihar Ashanti a wannan makon don jin tarihin Zango a jihar.

A hirarsa da Abdulmugeez Idi Kotoko, Sultan Umar Faruk sarkin zangon jihar Ashanti, ya ce unguwar Ramin Kura, nan ne zangon farko da aka fara kafawa a birnin Kumasi kuma hausawa ne suka kafa zangonnin Ghana.

Sultan ya kuma bayyana cewa bambancin unguwar Ramin Kura da sauran zangonni shi ne sana'oin da ake yi a wurin, akwai mayanka, madinka, 'yan koli masu saida kayan dabbobi a wannan zangon.

Duk da cewa hausawa mazauna zangonni da yawa a Ghana an haifesu tun ma kafin a kafa Ghana, har yanzu wasu na yi musu kallon baki, wani abu da ke ci wa hausawan tuwo a kwarya a cewar Sultan. Basaraken ya kuma yi kira ga gwamnati da ta dubi wannan batu.

Saurai cikakken shirin cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Da Dan Gari: Tattaunawa Da Sarkin Zango