Dakaru A kasar Afghanistan Sun Kaddamar Da Wani Aikin Bincike

  • Ladan Ayawa

Shugaba Hamid Karzai na Afghanistan daga hannun dama

Dakarun tsaro a gabashin Afghanistan sun kaddamar da wani aikin bincike na gano wasu ma’aikatan diflomasiyya biyu na Pakistan wadanda suka bace a lokacin da suke tuka mota zuwa Pakistan daga can shekaranjiya jumma’a.

Jami’an diflomasiyyar suna aiki ne a karamin ofishin jakadancin Pakistan dake Jalalabad, babban birnin lardin Nangarhar dake bakin iyaka da Pakistan din.

Kakakin gwamnatin lardin, Attahullah Khogyani, ya fadawa VOA cewa ana ci gaba da binciken wannan lamarin da ake zaton sace su aka yi, amma kuma bai bayyana matsayin da ake ciki ba.

A Pakistan, wani kakakin ma’aikatar harkokin waje yace gwamnati tana tuntubar hukumomi a birnin Kabul domin ganin an samo ma’aikatan diflomasiyyar nata cikin sauri kuma cikin koshin lafiya.

Nafees Zakaria ya ce hukumomin Afghanistan sun shaida musu cewa ana bakin kokarin binciken lamarin kuma an kafa wasu kungiyoyi uku na masu bincike domin tabbatar da cewa an samo jami’an cikin koshin lafiya.

Ya ki has ashen ko su wanene ke da alhakin bacewar jami’an diflomasiyyar nasu amma yace Pakistan ta bukaci gwamnatin Afghanistan da ta hukumta wadanda suka aikata wannan laifi abin kyama.

Har yanzu babu wanda ya fito ya dauki alhakin wannan lamarin.

Yayin da kungiyar Taliban ke da karfi da matsuguni a gundumomi da daman a lardin nagarhar, su ma magoya bayan kungiyar Daesh ko ISIS suna kara yawan ayyukan ta’addancin da suke gudanarwa cikin lardin.