Dakarun Iraqi Sun Sake Kwace Tashar Jiragen Saman Mosul daga Hannun ISIS

Rokar da dakarun Iraqi suka harba kan mayakan ISIS yayinda suke fafutikar kwato tashar jiragen saman birnin Mosul

Dakarun Iraqi dake samun tallafin sojojin Amurka sun kutsa cikin babban filin jiragen saman Mosul, wanda a baya ya kasance wani tunga na mayakan Daesh, ko ISIS.

A yau Alhamis dakarun tsaron, wadanda suka hada da ‘yan sandan tarayya da sojojin kai dauki cikin gaggawa da kuma zaratan sojoji masu yaki da ta’addanci, suka kutsa cikin filin jirgin da kuma wani sansanin soja dake nan kusa.

Kamfanin dillancin labaran Reuters yace gidan telebijin na Iraqi ya bada sanarwar cewa zaratan sojojin da kuma ‘yansandan tarayya sun kwace dukkan filin jirgin saman na Mosul suna rike da shi.

Farmakin da aka kai yau Alhamis a kan filin jirgin da kuma wannan sansanin soja, wadanda suke kan iyakar bangaren kudancin Mosul, wani bangare ne na wani gagarumin farmakin da aka kaddamar ranar Lahadin da ta shige da nufin fatattakar mayakan ISIS daga bangaren yammacin Mosul.

A watan da ya shige, sojojin Iraqi sun kwato bangaren gabashin birnin na Mosul daga ‘yan Daesh ko ISIS wadanda tun shekarar 2014 suka kama suka rike shi.