Dakarun Najeriya Sun Dakile Harin Boko Haram a Bama

Wani wuri da mayakan Boko Haram suka kai hari a arewa maso gabashin Najeriya

Rahotanni sun ce harin ya kai ga musayar wuta tsakanin dakarun Najeriya, lamarin da ya sa aka samu mace-mace a bangarorin biyu.

Mayakan Boko Haram sun kai wani hari akan dakarun Najeriya a Rann da ke karamar hukumar Kala-Balge a jihar Bornon kasar.

Rahotanni sun ce harin ya kai ga musayar wuta tsakanin dakarun Najeriya da maharan, lamarin da ya sa aka samu mace-mace a bangarorin biyu.

Harin ya faru ne a ranar Alhamis, amma hukumomin tsari ba su ce komai dangane da harin ba.

A daya bangaren kuma, dakarun kasar ta Najeriya, sun dakile wani hari na daban da ‘yan kungiyar ta Boko Haram suka kai a garin Bama.

Bama shi ne garin da kungiyar ta taba ayyanawa a matsayin hedkwatarta, ta kuma taba karbe ikonsa daga dakarun Najeriya.

Amma an kwato garin a watan Maris din 2015.

Jaridun Najeriya da dama da suka ruwaito labarin sun ce jama’ar garin na Bama sun yi ta murna bayan da aka fatattaki mayakan na Boko Haram.