Dakarun Nigeria Na Neman Janar Idris Alkali Wanda Ya Bace

Dakarun tsaron Nigeria

Dakarun Nigeria na ci gaba da neman Janar Idris Alkali wanda ya bace akan hanyarsa daga Abuja zuwa Bauchi ranar uku ga wannan watan a yakin Duradu cikin karamar hukumar Jos ta Kudu, jihar Plato.

Tun ranar uku ga wannan watan ne Janar Idris Alkali mai ritaya ya bace cikin jihar Plato wanda yanzu dakarun Nigeria suka dukufa wurin nemansa ko kuma gano gawarsa inda har ya mutu ne.

Shi Janar Alkali tsohon daraktan sadarwa ne a hedkwatar sojojin Nigeria dake Abuja kafin ya yi ritaya watan jiya.

Rahotanni na nuni da cewa Janar din ya bata ne cikin jihar Plato akan hanyarsa daga Abuja zuwa Bauchi.

Dakarun Nigeria a karkashin jagorancin Birgediya Janar Ibrahim Muhammad sun ce binciken da suka fara gudanarwa na nuni da cewar an gano motar Janar Idris Alkali a yankin Duradu dake karamar hukumar Jos ta Kudu. Saboda haka ne suke yasan wani tafki da suke zaton ciki aka jefa motar Janar din.

A cewar Birgediya Janar Ibrahim Muhammad sun shafe mako guda ke nan suna neman gawar Janar Idris Alkali da motarsa Toyota Corola baka. Ya ce muna so mu san ko yana raye. Ya ce suna da majiya kwakwara da ta fada masu cewar an tura wasu motoci cikin tafkin. Kwana uku ke nan suke kokarin gano wani abu daga cikin tafkin. Sai dai tafkin na da wahalar haka domin tsohon wurin hakan ma'adanai ne.

Birgediya Ibrahim Muhammad ya ce yanzu sun yanke shawarar yashe tafkin domin "mu gano abun dake kasarsa". Ya roki al'ummar dake yankin su ba su hadin kai wajen bankado bata gari a jihar tare da ba su tabbacin cewar jami'an tsaro ba zasu ci mutuncin kowa a yankin ba.

A halin da ake ciki kuma yayinda sojojin ke yasan tafkin, mata sanye da bakaken tufafi sun gudanar da zanga zanga saboda ruwan tafkin suke anfani dashi. Mary Yakubu jagorar matan ta ce idan sun yashe ruwan tafkin mazansu da 'ya'yansu na iya mutuwa saboda haka ba sa son kowa ya taba ruwan.

Duk da koken matan sojojin sun tsaurara matakan tsaro tare da ci gaba da yasan tafkin domin gano gawar Janar Idris Alkali ko akasin haka.

A saurari rahoton Zainab Babaji

Your browser doesn’t support HTML5

Dakarun Nigeria Na Neman Janar Idris Alkali Wanda Ya Bace - 2' 35"