Daliban Yadin Buni Da Ake Nema Konewa Suka Yi Kurmus A Dakunansu

Kwamitin da gwamnatin Yobe ta kafa ya gano cewa wasu daliban daga cikin wadanda aka hyi ta nema konewa suka yi, kuma an yi barna mai yawa a makarantar
Kwamitin da gwamnatin Jihar Yobe ta kafa domin bin sawun irin barnar da wasu 'yan bindiga suka yi cikin kolejin gwamnatin tarayya ta Yadin Bunim, ya yi tattaki zuwa cikin makarantar, inda ya gano cewa barnar da aka yi, ta shige misali.

Shugaban kwamitin, kuma kwamishinan shari'a na Jihar yobe, Barrister Ahmed Mustapha, yace sun gano cewa wasu daliban da ake ta nema a saboda ba a gansu cikin wadanda suka kubuta ko gawarwakin da aka samu ba, konewa suka yi a cikin dakunansu.

Yace binciken da suka yi ya gano cewa akwai wasu gawarwakin da ba a iya gane ko su wanene a saboda yadda suka kuna, amma kuma da yake an same su a kan gadaje ne a dakunan kwanan dalibai, an iya gano daliban dake cikin irin wadannan dakuna, da kuma gadajen da suke kwana a kai. Ta haka ne aka gano cewa su na daga cikin daliban da ake neman sanin abinda ya same su.

Barrister Ahmed Mustapha yace a yanzu, dalibai guda 4 ne kawai ba a san abinda ya same su ko inda suke ba.

Haka ma, 'yan bindigar da suka kai wannan farmaki sun kona gidajen malaman makarantar da ma kadarorinsu, babu abinda suka bari. Ajujuwa da ofisoshin makarantar duk an cunna musu wuta.

Your browser doesn’t support HTML5

Wasu Daliban Buni Yadi Da Ake Ta Nema, Konewa Suka Kurmus A Dakunansu - 2'51"