Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yobe ta Kafa Kwamitin Bin Diddigi da Tallafawa


Gwamna Ibrahim Gaidam, na Jihar Yobe, yana kallon wasu gawarwakin da aka kawo masallaci a Damaturu domin yi musu jana'iza.
Gwamna Ibrahim Gaidam, na Jihar Yobe, yana kallon wasu gawarwakin da aka kawo masallaci a Damaturu domin yi musu jana'iza.

Kwamitin zai duba barnar da aka yi a Yadin Buni tare da tallafawa wajen nemo daliban da aka ce har yanzu su na boye cikin daji a firgice

Kwamiti mai wakilai 10 da gwamnatin jihar Yobe ta kafa domin binciken irin hasarar rayuka da dukiya da aka yi a lokacin da wasu 'yan bindiga suka kai harin ta'addanci a kan Kolejin Gwamnatin tarayya dake Yadin Buni a karamar hukumar Gujba, ya fara gudanar da aikinsa na bin sawun barnar da aka yi.

Haka kuma, kwamitin yana hada kai da jami'an tsaro har ma da mafarautan gargajiya domin samo daliban da aka ce sun gudu cikin daji har yanzu ba su fito ba.

Shugaban kwamitin, Barrister Ahmed Mustapha, wanda shi ne kwamishinan shari'a na Jihar Yobe, ya ce kwamitinsu zai nazarci irin taimakon gaggawa da gwamnatin jihar zata iya bayarwa ga iyayen daliban da aka kashe da wadanda suka ji rauni. Haka kuma zasu dubi matakan da gwamnatin zata iya dauka na gaggawa domin taimakawa malaman makarantar da iyalansu.

Zasu kuma duba yadda zasu gyara abubuwan da aka lalata a makarantar.

Yace a wurin taronsu na farko jiya jumma'a, kwamitin ya yanke shawarar tuntubar jami'an tsaro da ku ma mutanen Sarkin Baka domin su binciko dajin dake kewaye da makarantar, musamman ma ta yamma da makarantar, inda aka yi imanin cewa akasarin dalibai sun gudu ta nan.
Gwamnatin Yobe ta Kafa Kwamiti Kan Harin da Aka Kai Yadin Buni - 3'41"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG