Dalilan Da Suka Sa Babangida Ya Fadi Zabe

Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja

A Jihar Niger a Najeriya, mutane na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu kan faduwar da gwamnan jihar da ya fadi a zabe.

Kasa da mako guda bayan da gwamnan jihar Niger Babangida Aliyu ya fadi a zaben ‘yan majalisar dattawa, mutanen jihar na ci gaba da bayyana ra’yoyinsu.

Dan takarar APC David Umaru ne ya kayar da gwamnan lamarin da ya zo mutane da dama a kasa baki daya.

“Ya taka sarakai, baya ganin girman sarakai bay a ganin girman da Allah ya musu, na biyu ya nuna cewa kamar karfin gwamnati ne zai kasha wurinan.”

Sai dai masu sharhi akan harkokin siyasa na ganin ba haka lamarin ya yake ba, a cewarsu gwamnan ya juya wa mutanen jihar baya.

“Akwai matsaloli da yawa, na farko shi ne alkawari idan ka yiwa mutane alkawari idan ka yiwa mutane alkawari ka cika.” In ji Ahmad Dogara.

Tuni dai gwamna Aliyu y ace ya rungumi kaddara kan wannan kayi da ya sha, inda y ace ai da bai san cewa ma zai zama gwamna ba.

“Mutumin da kana bacci Allah ya tashe kay a ce kazoo ka yi gwamna shekara takwas, don kai a ganin ka kana so ka zama sanata Allah ya ce a’a ban yi niyyar b aka wanna ba, sai ka yi fushi, to ka ko zama mahaukaci in ka yi fushi.

Your browser doesn’t support HTML5

Dalilian Da Suka Sa Babangida Ya Fadi Zabe - 2'50"