Dalilin Da Ya Sa Trump Ya Hana Ukraine Kudaden Tallafi Miliyan 400

Mick Mulvaney

Fadar White House ta yarda a jiya Alhamis cewa shugaban Amurka Donald Trump ya dakatar da ba da tallafin dala miliyan $400 da dakarun Ukraine ke matukar bukata, don nuna matsin lamba ga Ukraine ta binciki ‘yan jam’iyyar Democrats da zaben shugaban kasa da aka yi a shekarar 2016.

Wannan sabon bayani mai cike da abin mamaki ya fito ne daga bakin mukaddashin shugaban ma’aikatan fadar White House, wato Mick Mulvaney, bayan da Trump ya kwashe makonni yana musanta cewa akwai batun ba-ni gishiri-in-ba-ka manda a tsakaninsa da Ukraine.

Mulvaney ya fadawa manema labarai a Fadar White House cewa, an dakatar da kudin kasar ta Ukraine ne saboda damuwar da Trump ya nuna kan matsalar rashawa a kasar, da kuma zargin cewa Ukraine na da hannu a cikin zargin da Amurka ta ke yi wa Rasha na yin kutse a sakonnin email din kwamitin gudanarwa na jam’iyyar Democrat a shekarar 2016.