Dan Atiku Abubakar Zai Auri ‘Yar Nuhu Ribadu

Aliyu Atiku Abubakar da Fatima Nuhu Ribadu

Aliyu Abubakar, dan tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyar PDP a zaben da aka gudanar a shekara ta 2019 Atiku Abukar, zai auri Fatima ,‘yar tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa Nuhu Ribadu, ranar asabar.

Za a daura auren Aliyu, wanda shi ne dan tsohon mataimakin shugaban kasar na uku, da Fatima ‘yar shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa na farko, a gidan Nuhu Ribadu da ke wata unguwar masu hali a birnin tarayya Abuja. Bisa ga takardar gayyatar da aka buga, za a daura auren ne a gidan dake lamba 18 titin Mambilla, Aso Drive da karfe goma sha daya na safe.

Bayanai na nuni da cewa, mutane kalilan ne aka gayyata sabili da kiyaye dokar rage cunkoso biyo bayan barkewar cutar Coronavirus.

Katin gayyatar auren Aliyu Abubakar da Fatima Nuhu Ribadu

Aliyu shine dan Alhaji Atiku Abubakar na uku, kuma dan matar Atiku ta uku Rukaiyatu ‘yar Lamidon Adamawa, Aliyu Musdapha. Banda gadon sunan kakansa, Aliyu ya kuma gaji sarautar mahaifinsa Turakin Adamawa bayanda aka nada Alhaji Atiku Abubakar a matsayin Wazirin Adamawa.

Atiku Abubakar da dansa Aliyu Atiku Abubakar

Amaryar Fatima Ribadu, ta kammala makarantar sakandare a Turkish International da ke in Abuja a 2015 kafin ta tafi Ingila inda ta yi karatun jami’a.

Aliyu Atiku Abubakar da Fatima Nuhu Ribadu

Fatima ‘yar matar Nuhu Ribadu ce Zarah, wadda mahaifinta wani fitaccen Farfesa da kuma dan siyasa Iya Abubakar.ne a jihar Adamawa.

Babu tabbacin yadda ma’auratan suka hadu ko da yake dukansu suna da zama a Abuja. Duk da yake dukansu sun fito daga jihar Adamawa, suna jam’iyu dabam dabam, kuma a fili ya ke sun dade da raba gari tun suna aiki tare a gwamnatin shugaba Olusegun Obasanjo lokacin uban ango, Alhaji Atiku Abubakar yake mataimakin shugaban kasa, Nuhu Ribadu kuma yana matsayin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa.

yan-najeriya-na-ci-gaba-da-sukar-gwamnati-kan-bukin-hanan-buhari

A watan jiya Aisha Hanan, 'yar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta auri wani hadimin gwamnati Muhammad Turab Sha’abab a wani kayataccen bukin da ya dauki hankalin 'yan Najeriya inda da dama suka yi ta sukar yadda aka rika facaka da kudi a daidai lokacin da talakawa suke fama da kuncin rayuwa da ta kara ta'azzara sabili da bullar cutar Coronavirus.