Dan Takarar Jam'iyyar Democrat Joe Biden Zai Kai Ziyara Kenosha

Masu zanga-zanga a Kenosha, Wisconsin

Dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar Democrat Joe Biden zai yi balaguro zuwa garin Kenosha da ke jihar Wisconsin a Amurka, inda zai gana da al’ummar yankin.

Kwamitin yakin neman zaben Biden ya ce ganawar da za a yi a birnin mai mutane 100,000 da ke gabar tafkin Michigan, za a yi ta ne “don hada kan Amurkawa da kuma duba yadda za a tunkari kalubalen da ake fuskanta.”

Wannan ziyarar ta Biden ta zo ne bayan ziyartar garin da Shugaba Trump ya yi inda ya zagaya wani titi da aka lalata gine gine a lokacin zanga-zangar da aka yi biyo bayan harbin wani bakar fata da wani dan sanda farar fata ya yi.

A ziyarar da Trump ya kai Kenosha, ya yi amfani da wannan damar don jaddada goyon bayan shi ga jami’an tsaro, inda ya ce “dole ne su warware matsaloli, kana dole ne su yi tsayin daka, kuma dole ne ka kasance da niyar kawo jami’ai, kamar dogarawan wanzar da zaman lafiya na kasa don kwantar da tarzoma.